Tabbatar da gaskiyar Labari ko akasinsa, bai kamata yayi wahala ba a zamanin AI
Sannan akwai amintattun kafafen yaɗa Labarai da ake samun kowani Labari mai tushe daga wajensu
A Hadisi ɗaya aka haramta jinin Musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa
Mutunta abokin saɓani ba zaɓi ba ne, ba kuma alfarma ba ce
Wajibi ne!
Abu Ramzi
Kamashi alama ce ta fara bayyana ķudurorin haɗakar biyayya ga manufofin Gwamnatin Israel
Kuma mari ne a fuskar Musulman Nigeria da duk masu ƙiyayya da ta'addanci da ake ganawa Falasɗinawa a Gaza
Idan kuna son taimakon maƙiyanku cikin nasara a kanku, to ku mayar da hankalinku, ku ƙarar da ƙarfinku cikin yaƙar junanku
Dole ne ni da kai, mu haɗu mu kawo ƙarshen wannan wawancin na sheƙar da jinin junanmu da sunan ɗaukar fansa.
Idan Hutu da Tutsi a Rwanda sun iya, me zai hana ni da kai mu iya..
Dole mu yi wannan aikin, kuma dole mu ƙaddamar dashi akan sauran aiyuka domin wanzuwarmu.
Makirci da baƙin zalumcin da Ƙasashen Musulmai ke fuskanta a Gabas ta tsakiya, bashi da nisa da mu a Yammacin Africa.
Gwargwadon yanda muka fahimci wannan da wuri, kuma muka yi aiki domin hana tabbatar gurace-guracensu, gwargwadon yanda muka ceci kawunanmu.
Ba zaka iya aiwatar da duk ƙudurorinka ba
Hanya ƙwara ɗaya ta wanzuwar kyawawan aiyukanka, ita ce samar da wani ko wasu irinka
Wajibine Gwamnati ta gaggauta hukunci mai tsanani akan waɗanda ke da hannu a cikin abinda ake fada na cewa, ana ɗaukan yaran Musulmai daga makarantun Gwamnati ana kaisu wani waje domin canza masu Addini, idan ya inganta.
Shiru da kawaici fa, ba tsoro ba ne!
Kada tsanar mafi yawan mutane ta dameka, sau da yawa alama ce ta bijirewa soye-soyen rayukansu.
Ka tuna cewa mafi yawan waɗanda a yau muke tutaya dasu, mafi yawan mutanen zamaninsu sun tsanesu
Wajibinmu shine bibiyar hanyar magabata cikin mu'amala da Nassi, amma ba taƙaituwa da fahimtarsu ga Nassi ba;
Matuƙar ba Ijma'i suka yi cikin fahimtar ba.
Karatun Saheehul Bukhari - 25/02/2024 - Darasi na 25 a Kitabul Hajj xitter.cf/i/broadcasts/1zqKVqzjA…
Karatun Muwaɗɗa Malik 17-02-2024 xitter.cf/i/broadcasts/1mnxepkaM…







